Rundunar ƴan sandan Nijeriya shiya ta ɗaya dake Kano, ta samu nasarar kama wani mai suna, Richard Peter mai shekaru 32 ɗan asalin jihar Legos, tare da ƙwato wayoyin salula guda 29 da sauran kayayyaki da ake zargin ya sace wa ɗalibai mata a jami’ar Bayero Kano bayan wata damfarar aiki ta bogi.
Kakakin rundunar shiya ta ɗaya, DSP Abdullahi Hussaini, ya bayyana cewa, a ranar 12 ga watan Mayu 2026 suka samu ƙorafi daga wasu ɗalibai ƙarƙashin jagorancin, Clementina Paul, inda suka zargi mutumin da damfararsu da sunan samar musu da aiki na bogi.
Binciken farko ya tabbatar da cewa wanda ake zargin yabi ta hannun wata mai suna, Faith Dauda, inda ya gayyaci mata 38 zuwa wani Hotel a unguwar Sabongari Kano, a ranar 10 ga watan Mayun 2026, sannan yayi musu ƙaryar cewa ba za a yarda da wayoyin hannun ba, a wajen aikin inda umarce su su ajiye da sauran kayayyakinsu.
DSP Abdullahi Hussaini, ya ƙara da cewa daga bisani wanda ake zargin ya yiwa matan odar abinci na naira dubu shida (N6,000) kowacce daga cikinsu amma yabar wurin tare da ya biya ba.Sai dai matan sun gano cewar ya koma ɗakin lokacin da suke cin abincin ya sace wayoyinsu da sauran kayayyakinsu baki ɗaya, inda binciken sirrin da ƴan sandan su gudanar ya sanya aka gano ɗaya daga cikin wayoyin, a tashar mota ta Kano-Line, amma kafin aje motar da ya shiga don zuwa Legos ta tafi inda aka samu nasarar kama shi a Zaria dake jihar Kaduna.
Jami’an ƴan sandan sun ƙwato wayoyin salula guda 29 da sauran kayyakin da ya sacewa matan, inda yanzu haka yake tsare a sashin binciken manyan laifuka na shiya ta ɗaya kafin gurfanar dashi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Mataimakin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, AIG Garba Ahmed, ya yabawa jami’an ƴan sandan da suka gudanar da aikin cikin gaggawa tare da yin amfani da bayanan sirri, ya kuma sake jaddada ƙudirin rundunar ƴan sandan shiyya ta ɗaya don kare al’umma daga damfara da sauran laifuka.
AIG Garba, ya shawarci jama’a su kasance masu takatsantsan da tayin aiyukan da ba a tantance sahihancinsu ba, sannan kuma a rinƙa gaggauta kai rahotan duk wani abu da zargi zuwa ofishin ƴan sanda mafi kusa.