Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya naɗa Dakta Olugbemisola Titilayo Odusote, shugabar makarantar horar da Lauyoyi ta Najeriya.
Wannan naɗi na nufin cewa ta zama mace ta farko da za ta jagoranci makarantar tun bayan kafa ta a shekara ta 1962.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce naɗin zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Janairun, 2026 na tsawon shekara huɗu.
Dakta Odusote mai shekara 54, ita ce mataimakiyar shugabar makarantar a halin yanzu.
Sanarwar ta ce Odusote za ta gaji shugaban makarantar ta horar da lauyoyi mai barin gado, Farfesa Isa Hayatu Chiroma wanda wa’adinsa zai kare ranar 9 ga watan Janairun, 2026, bayan shafe tsawon shekara takwas.
