Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa shugabannin sabuwar Hukumar Raya yankin Arewa-maso-yammacin Najeriya.
Bola Ahmad Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dattawa sunayen shugabannin sabuwar Hukumar Raya Yankin Arewa-maso-yamma domin samun sahalewarsu.
Wannan na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta kafa hukumar da shugaban ƙasa ya yi a ranar 24 ga watan Yulin 2024.
Shugabannin da shugaban ƙasa ya miƙa sunayensu ga Majalisar su ne:
Shugaba: Ambassador Haruna Ginsau (Jigawa)
Manajin darakta: Professor Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano)
Sauran lambobin hukumar:
– Dr. Yahaya Umar Namahe (Sokoto)
– Hon. Aminu Suleiman (Kebbi)
– Sen. Tijani Yahaya Kaura (Zamfara)
– Hon. Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
– Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil (Kano)
– Shamsu Sule (Katsina)
– Nasidi Ali (Jigawa)
Ana sa ran wannan sabuwar hukuma za ta mayar da hankali wajen samar da cigaba ga ɓangaren tattalin arziƙi da bunƙasa rayuwar al’ummar wannan yanki.
Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga wacce ya fitar a yau 28 watan Satumba, 2024.