Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami babban shugaban hukumar tattara haraji ta ƙasa Muhammad Nami.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya tabbatar da hakan a cikin wata saanarwa, sannan yace haka kuma har Mista Tinubu ya naɗa Zacch Adedeji a madadinsa.
A cewar sanarwar , har wa yau Mista Tinubu ya umarci Mista Nami ya hanzarta ya fara hutun wata uku nan take kafin ya cika lokacin yin ritaya kamar yadda dokar ma’aikatan gwamnati ta yi tanadi. Daga hutun Mista Nami zai zarce ritaya a ranar 8 ga watan Disamban shekarar nan ta 2023.
Ngelale yace saboda haka an naɗa Adedeji shugaban riƙo na tsawon kwanaki 90 kafin a tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaban hukumar tattara harajin ta ƙasa a wa’adin shekaru huɗu a matakin farko.
Adedeji ya kammala digirorinsa a ilimin lissafin kuɗi da sakamakon farko a Jami’ar Obafemi Awolowo.
A can baya Adedeji ya riƙe muƙamin mai bai wa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin haraji, kafin nan ya yi kwamishinan kuɗi a jihar Oyo kuma ya taɓa zama babban shugaban hukumar da ke kula da wadata ƙasa da sukari.