Home » Tsohon Gwmnan Kano Ya buƙaci ‘Yan Siyasa Su Gina Al’umma Ba Sace Kuɗin Ƙasa Ba

Tsohon Gwmnan Kano Ya buƙaci ‘Yan Siyasa Su Gina Al’umma Ba Sace Kuɗin Ƙasa Ba

by Anas Dansalma
0 comment
Tsohon Gwmnan Kano Ya buƙaci 'Yan Siyasa Su Gina Al'umma Ba Sace Kuɗin Ƙasa Ba

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bukaci ‘yan siyasa su gina jama’a maimakon sace dukiyoyinsu.

Ya yi wannan nasihar ne a Minna a jiya Alhamis a lokacin da ya zama shugaba a wajen taron kaddamar da zababben gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago.

Tsohon gwamnan ya bukaci zababben gwamnan da ya maida hankali sosai a fannin ilimi da tsaro domin amfanin jihar Neja ko kuma zai yi nadama a nan gaba.

Ya kara da cewa jarin da ake zubawa a fannin ilimi na iya yiwuwa ba za a ga tasirinshi ba nan take,  amma a karshe za a ga sakamako mai dimbin yawa.

Ya kara da cewa, Bago ya zama gwamna mai taka rawar gani, dole sai ya kama aiki tukuru bayan an rantsar da shi don cigaban tattalin arziki da jin dadin zamantakewar al’ummar jihar.

Ya bayyana cewa rashin aiki da ilimi ya sa gwamnoni da dama ba su da wani abin a zo a gani a jihohinsu, bayan shekaru hudu ko takwas na mulki da suka yi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?