Asussun Tallafawa ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na gudanar da taron wayar da kai na kwana biyu da wakilan kafafan yaɗa labarai na jahohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna, da nufin samar da hanyoyin ƙarfafa muryar yara domin mahukunta su ɗau matakan kulawa da kuma kare haƙƙoƙinsu.
Jami’in hulɗa da Jama’a na UNICEF mai kula da jahohin Kano da Jigawa da Katsina, Mista Samuel Kaalu ya ce maƙasudin taron shi ne jan hankulan kafafen yaɗa labarai wajen bai wa buƙatun yara muhimmanci a kafofinsu da kuma fito da matsalolin da yara ke fuskanta a waɗannan jahohi da nufin magance su.
Mr. Samuel Kaalu ya yaba da irin gudunmawar da kafafan yaɗa labarai ke bayarwa wajen ganin Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara (UNICEF) ta cimma manufofinta.
Wasu daga cikin Gidajen yada labarai da suka halarci taron sun hada da: gidan Rediyon Kano da Muhasa da Aminci rediyo da Arewa da Legend FM Daura da gidan talbijin na NTA Kano da na Katsina da gidan jaridar Punch.