UNICEF ta nuna shakunta game da shawo kan yawan bayan gida a sarari a Najeriya

Asusun Tallafawa wa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ta ce da wahala Najeriya ta iya kawo ƙarshen matsalar bayan gida a sarari nan da shekarar 2025.

UNICEF ta ce jan ƙafar da ake wajen ɗaukar matakan da suka dace wajen cimma wannan muradi.

Jami’i na musamman da ke ofishin UNICEF  a Najeriya reshen jihar Legas, Monday Johnson, ne ya bayyana hakan a jiya a garin Ibadan a yayin wani taron kwana biyu da manema labarai na Kudu maso Yammacin ƙasar nan.

Ya ce jihar Jigawa ce kaɗai ta zama zakaran gwajin dafi da za a ce ba ta fama da matsalar yawan bayan gida a sarari.

Sannan ƙananan hukumomi 105 ne cikin 774 da ake da su a ƙasar nan, su ne aka tabbatar ba su da wannan matsala ta yawan bayan gida a sarari.

A cewarsa, idan aka cigaba da tafiya a yadda ake a yanzu, Najeriya za ta iya rabuwa da wannan matsala ne kaɗai nan da shekera ta 2046.

Ya kuma shawarci ‘yan jarida da su cigaba da wayar da kan al’umma kan illar yin bayan gida a sarari tare da samar da rahotanni na kawo mafita kan wannan matsala domin ƙarfafa wa gwamnati cigaba da ɗaukar matakan da suka dace.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr