Wani mai haɗa wa ƙungiyar Boko Haram, mai suna Awana Gaidam ya rasa ransa bayan ya yi kuskuren taka wani bam da ya binne wa dakarun ƙasar nan domin ya tashi da su, wanda nan take bam ya tashi da shi.
An rawaito cewa Awana Gaidam ya taka bam ɗin da ya haɗa da hannun nasa ne a jihar Borno.
An tabbatar da cewa bayan matsayin da Awana mai shekaru 39 yake da shi na musamman a ƙungiyar ta Boko haram, shi ne yake haɗa musu nau’o’in makamai masu fashewa.
Ana ganin cewa Awana shi ne da alhakin hare-haren da aka kai wa dakarun Operation Haɗin Kai ta hanyar saka musu makamai masu fashewa a yayin ran gadinsu a manyan hanyoyin Maiduguri zuwa Damboa, da Bama zuma Pulka da kuma Banki zuwa yankin Darajamal.
Wani rahoto ya tabbatar da cewa bam ɗin ya tashi da motarsa ne a wajenjen Njumia da Arra a dajin Sambisa, wanda yai sanadin mutuwarsa nan take.