Rundunar yan sandan jihar Kano ta gurfanar da matashiyar yar Tiktok dinnan mai suna, Rukayya Ibrahim, wadda akafi sani da Ummin Mama, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake hukumar hisbah, bisa zarginta da yada faifen bidiyon tsiraici a shafin Tiktok.
An gurfanar da matashiyar dauke da tuhume-tuhumen, aiyukan nuna tsiraici, da shigar banza da kuma yada wakokin fitsara.
Bayan karanto mata kunshin tuhumar da ake yi mata, nan ta ke ta amsa laifukan.
Alkalin kotun mai shari’a, Sani Tamim Sani Hausawa, ya aike da ita zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya zuwa ranar juma’a 21 ga watan Maris 2025, domin yi mata hukunci.
- Tinubu ya rantsar da mai riƙon muƙamin gwamnan jihar Rivers
- Tinubu ya rantsar da mai riƙon muƙamin gwamnan jihar Rivers
To sai dai bayan aike wa da ita zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, alkalin kotun ya samu kiraye-kirayen mutane da dama cikinsu harda wanda ya yi masa tayin cin hanci na Dalolin Amurika, wai don ya saki matashiyar amma alkalin kotun yaki karbar tayin cin hancin inda ya yi fatali dashi.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ce ta kama wata Rukayya Ibrahim, bisa zargin ta da yaɗa hotunan tsaraicin a dandalin TikTok.
Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbar na jihar Kano, Dakta Mujahedden Aminudden Abubakar, ya ce kama matashiyar Ummin Mama da suka yi, ya biyo bayan korafe-korafen da suka samu kan yadda ta ke yada tsiraici a shafin Tiktok, wanda hukumar ta ce yin hakan ya saba da shari’ar addinin musulinci da kuma al’ada.