Wani raho bayyana yadda Malami ɗaya ke kula da ɗalibai 105 a makarantun gwamnatin Kano.

Wani rahoton ƙididdigar makarantu na shekarar karatu ta 2024/2025 ya nuna cewa makarantun gwamnati a Jihar Kano na fama da ƙarancin malamai da azuzuwa, inda malami ɗaya ke kula da yara har 105 a makarantun firamare .

Rahoton, wanda ma’aikatar ilimi ta jihar ta tabbatar shi ne sabon rahoton hukuma mafi inganci duk da cewa an fitar da shi tun watan Disamban 2025, ya nuna cewa duk malami daya ya na kula da ɗaliban makarantun firamare guda 105, abin da ya zarce ƙa’idodin samar da ilimi na ƙasa da na duniya.

Rahoton ya kuma nuna cewa a ƙananan makarantun sakandare, malami ɗaya ya na kula da ɗalibai kusan 50, yayin da a manyan makarantun sakandare adadin ya kai ɗalibai 37 ga malami ɗaya.

UNESCO na ba da shawarar kada ɗalibai su wuce 25 a duk aji a makarantun firamare.

Haka kuma, manufofin ilimi na Najeriya sun tanadi rabon malami da ɗalibai da ya fi haka ƙanƙanta a matakan makarantu daban-daban.

Rahoton ya danganta wannan lamari da ƙaruwar dalibai da ake samu a makarantu.

Ya ce a lokacin da aka gudanar da ƙididdigar, ɗalibai miliyan 5.69 ne ke karatu a makarantun gwamnati na jihar.

Cikinsu akwai dalibai 683,773 a ƙananan azuzuwan firamare, miliyan 4.03 a makarantun firamare, 509,314 a ƙananan makarantun sakandare, 412,518 a manyan makarantun sakandare, 31,236 a makarantun kimiyya da fasaha, da kuma 19,049 a cibiyoyin koyon manya da ilimin da ba na boko ba.

Rahoton ya ce kara yawan wadanda ake sawa a makarantun ne ya jawo matsin lamba kan malamai, azuzuwa da sauran kayayyakin koyarwa, lamarin da ke haifar da damuwa kan ingancin koyo da koyarwa.

Cunkoso a azuzuwa da ƙarancin bandakuna

Rahoton ya kuma nuna cewa azuzuwan makarantun gwamnati na Kano na fama da cunkoso dalibai.

A cewarsa, akalla yara 145 ne ke amfani da aji ɗaya a matakin firamare, a kananan makarantun sakandire akan sami dalibai 78 a makarantu, yayin da ake samun dalibai 69 a manyan sakandare.

Har ila yau, dalibai 342 kan yi amfani da bandaki guda a makarantun firamare, yayin da adadin ya kai 122 a ƙananan sakandare da dalibai 73 ke amfani da bandaki daya a manyan makarantun sakandare.

An gudanar da ƙididdigar ne a makarantun firamare 7,331, da ƙananan makarantun sakandare 1,451,sai manyan makarantu sakandare 800, da makarantun kimiyya da fasaha 49, da cibiyoyin koyon manya 63 a faɗin jihar.

Sanya ya’ya mata a makarantu ya karu a Kano

Duk da waɗannan ƙalubale, rahoton ya nuna cewa an samu ci gaba wajen yawan zuwa makaranta, musamman ga ‘ya’ya mata.

A cewarsa, ‘yan mata sun kai kashi 52 cikin 100 na ɗaliban firamare, 56 cikin 100 a ƙananan sakandare, da 54 cikin 100 a manyan sakandare.

Rahoton ya kuma bayyana cewa malamai 45,007 ne ke aiki a makarantun gwamnati na jihar a matakai daban-daban, inda mafi yawansu ke koyarwa makarantun firamare.

Gwamnati ta ce tana ɗaukar matakai

Da yake mayar da martani kan rahoton, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Ali Haruna Makoda, ya amince cewa akwai ƙalubale, amma ya ce gwamnati ta fara aiwatar da matakai da dama domin inganta fannin ilimi.

Ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da Ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta kai jihar domin duba ayyukan shirin AGILE.

A cewarsa, gwamnatin jihar ta bayar da kwangilolin da darajarsu ta haura naira biliyan 24 domin gina sabbin makarantu 49, tare da shirye-shiryen gyaran makarantu 300 a dukkan mazabu jihar 484.

Makoda ya ce gwamnatin jihar ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi tun shekarar 2023 saboda matsalolin da suka samo asali sakaci a baya.

KADAURA24

Post masu alaƙa

Hukuncin kotu kan jam’iyyar NDC koma baya ne ga dimokraɗiyya – PDP

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta kafa kwamitin da zai nemo hanyoyin da jami’anta za su mallaki gidaje.

Kotu ta ba da umarnin kama tsohon minista Uche Nnaji kan zargin Jabun takardu na makaranta