Jam’iyyar PDP tsagin Tanimu Turaki ta nuna damuwa kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke kan soke rijistar jam’iyyar NDC, inda ta ce hakan koma baya ga dimokuraɗiyya a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na riƙo, Ini Ememobong, ya fitar, PDP ta ce ko da yake tana jiran samun cikakken bayani dangane da hukuncin kotun, ta yi alawadai da abin da ta kira “murƙushe dimokuraɗiyya” a ƙasar.
Jam’iyyar ta ce hukuncin ya zo ne bayan ƴan Najeriya da dama sun kashe kuɗaɗe domin neman muƙaman siyasa a ƙarƙashin NDC.
“Wannan hukunci ba wai yana takaita tsarin jam’iyyu ba ne kawai, yana haifar da asara ga ƴan Najeriya da suka sa rai a jam’iyyar,” in ji sanarwar.
PDP ta kuma zargi gwamnatin ƙasar ƙarƙashin jam’iyyar APC da ƙoƙarin dakushe jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, domin bai wa Tinubu damar sake tsayawa takara ba tare da wani ƙalubale.
Jam’iyyar ta buƙaci shugabannin NDC su ƙalubalanci hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta daina abin da take yi domin zaman lafiya da kuma tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya a ƙasar.