Kotu ta ba da umarnin kama tsohon minista Uche Nnaji kan zargin Jabun takardu na makaranta

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da sammacin kama tsohon Ministan Ƙirƙire-ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, bisa zargin gabatar da jabun takardun karatu da na aikin bautar ƙasa (NYSC).
Hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ce ta samu umarnin kama Nnaji bayan ta shigar da ƙara a kotun tarayya ƙarƙashin lamba FHC/ABJ/CS/1160/2026.
An naɗa Nnaji a matsayin minista ne a watan Agustan 2023 daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Sai dai daga bisani ya yi murabus bayan zarge-zargen cewa ya gabatar da jabun takardun karatu da na NYSC yayin tantancewarsa da tabbatar da naɗinsa.
Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya shaida wa kotu cewa hukumar ta nemi wannan umarni ne saboda Nnaji ya ƙi amsa gayyatar da aka yi masa domin gudanar da bincike kan zargin da ake masa.
Hukumar ta kuma roƙi kotun da ta ba ta damar ayyana Nnaji a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo ta hanyar jaridu, kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin yaɗa labarai, tare da ba jami’an tsaro da ma fararen hula ikon kama shi su miƙa shi ga ICPC domin bincike

Post masu alaƙa

An yi garkuwa da ɗalibai a hanyar zuwa jarrabawar JAMB

Mai Ilimi na gaske ba ya Fariya ko dagawa – Sarki Aminu Ado Bayero

Sojoji sun daƙile yunƙurin mahara da kashe kwamanda a Borno