Tsohon dan tawaye kuma dan siyasa a Jamhuriyar Nijar, Rhissa Ag Boula, ya kaddamar da wata kungiya da za ta yi fafutukar ganin an mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.
Boula ya kaddamar da kungiya mai suna the Council of Resistance for the Republic (CRR) domin neman goyon baya daga kasashen duniya don mayar da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
Wannan wata alama ta nuna turjiya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a karshen watan jiya.