Home » Wasu Fusatattun Matasa Sun Ƙone Gidan Mawaƙi Rarara

Wasu Fusatattun Matasa Sun Ƙone Gidan Mawaƙi Rarara

by Anas Dansalma
0 comment

Wasu matasa a nan jihar Kano sun cinna wa gidan ofishin mawaƙi  Kahutu Rarara wuta

Wannan al’amari ya faru ne a cikin ƙasa da sa’a ɗaya da sanar sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kano wanda aka ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Wani ganau ba jiyau ba, wanda ke zaune kusa da inda abin ya faru mai suna Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa,

fusatattun matasan sun yi wa gidan na Rarara dirar mikiya tare da cire abubuwan amfani kafin daga bisani su cinna wa gidan wuta.

jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin korar waɗannan matasa daga wajen,

sai dai wutar ta cigaba da ci kuma har zuwa sanda majiyarmu ke haɗa wannan rahoto, jami’an kashe gobara ba su kawo ɗauki ba.

Rarara dai mawaƙi ne da aka fi sani a matsayin mai mara wa jam’iyyar APC baya musamman a mataki na ƙasa, sai dai a cikin daren jiya an ga wata sabuwar waƙa na yawo wanda mawaƙin ya yi wa Abba Kabir Yusuf.

Har yanzu dai ba kai ga gano dalilan da suka tunzura waɗannan matasa zuwa gidan mawaƙin ba, sai dai ana ga koma mene ne, dalilin ba zai wuce na siyasa ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?