Hukumar Bunƙasa Yankin Arewa-maso-gabas, wato North East Development Commission, ta kai kayan agajin gaggawa ga mutanen da suka gamu da ibtila’in gobara a sansanin ‘yan gudun Hijrah na Rundaben Shuwa da ke kusa da Bauchi.
Wannan al’amari ya faru ne a lokacin da ake sallar juma’a bayan da wata mummunar gobara ta tashi daga wani gida inda ta wutar ta watsu zuwa wasu gidajen a ƙalla 20 waɗanda yawanci gidajen kara ne, tare da ƙone su kurmus.
Sama da mutane 100 ne suka tagayyara sakamakon wannan gobara, inda wasu suka koma bukkokin ‘yan uwa da je sansanin da barandar masallaci domin zama da iyalansu kafin isowar kayan agaji.
Ga Mu’azu Hardawa Bauchi da cigaban wannan labari:
Bayan kashe wutar, an yi jana’izar wani magidanci wanda ya rasa ransa, a ƙarƙashin jagorancin tawagar shugaban ‘yan gudun Hijra Buba Musa Shehu, tare da binne shi a makabartar Dungulbe.