Wasu ‘yan bindiga a sanyin safiyar nan sun kai wani sabon hari garin Dogon-noma da ke ƙaramar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki uku bayan kashe wani mutum ɗaya da yin garkuwa da mutane 8 a garin Banono Angwaku da ke ƙaramar hukumar ta Kajuru.
Tsohon shugaban ƙaramar hukumar, Cafra Caino, ne ya tabbatar da kai wannan hari ga manema labarai.
A cewarsa, masu kai harin sun kai samamen ne da asuba tare da yin harbe-harben kan mai uwa dawabi.
A yayin da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, kan wannan al’amari, ya sanar da majiyarmu kan cewa su turo masa da saƙon kar ta kwana saboda yana tuƙi, amma har zuwa sanda muke haɗa muku wannan rahoto bai kai ga yi mana ƙarin haske ba.
Ƙananan hukumomin Kajuru da Chikun na jihar Kaduna dai su ne kan gaba a ‘yan kwanakin nan wajen fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.