Wata kotu a jihar Kano ta samu wani tela da laifin gurɓata muhalli saboda karar da keken dinkin sa .
Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar ce ta kai ƙarar telan mai suna Mubarak Yusuf, kan yadda keken ɗinkinsa da kuma injin janareto ke damun mutanen anguwar da yake da daddare.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce duk da cewa ya musanta zargin, amma ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da kotun.
- Gwamnan Kano Ya Yi Alkawarin Samar Da Ofishin Kashe Gobara A Kasuwar Farm Center.
- Kotu Ta Aike Da Dan TikTok Din Da Ke Wanka A Kan Titi A Kano Gidan Yari
Har ila yau, kotun ta kai ziyarar gani da ido shagon da telan yake aiki, inda kuma ta tabbatar da cewa karar kekensa yana hana mutane bacci da daddare, abin da ya saɓa wa sashi na 7 na dokar kare lafiyar al’umma ta 2019.
“Don haka ne kotun ta yanke hukuncin taƙaita masa lokutan yin aiki, inda yanzu zai riƙa aiki daga karfe 6:00 na safe zuwa 9:00 na dare,” in ji sanarwar.
Kwamishinan muhalli na jihar ta Kano, Dakta Dahir Hashim ya yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya ƙara nanata zimmar ma’aikatar na ganin ta tabbatar da cewa kowanne mutum ko kuma wuraren kasuwanci sun bi matakan kare lafiyar al’ummar da kuma muhalli.