WATA MA’AKACIYAR LAFIYA Asmau Lawali Bungudu, da ke aiki a Asibitin Ahmed Sani Yariman Bakura da ke Gusau a Jihar Zamfara, ta yanke jiki ta fadi, inda daga nan ta ce ga garinku nan.
Rahotanni sun ce, marigayiya Asma’u ta kasance cikin bacin rai a lokacin da ta fito bakin aiki da sanyin safiyar Laraba.
Jami’in hulda da jama’a na asibitin kwararru na Ahmed sani Yarima, Auwal Usman ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ma’aikaciyar jinya Asmau tana bangaren NHIS Clinic ne kuma ta duba majinyata kusan 30 a yau kafin ta kai kanta ga Likita don bayyana masa damuwar da ke damunta a zuciya.
A cewarsa, bayan Marigayiya Asma’u ta bayyana damuwarta ga likita, likitoci ba su yi kasa a guiwa ba domin ceto rayuwarta amma lamarin ya cutura, ta yanke jiki ta fadi ta ce ga garinku nan.
Jami’in hulda da Jama’a na Asibitin ya bayyana cewa tawagar gudanarwar asibitin karkashin jagorancin Daraktan Likitoci Dr. Usman Muhammad Shanawa sun mika gawar Asma’u ga ‘yan uwanta don yi mata jana’iza kamar yadda addininta ya tanada.