• Home  
  • Ya Kamata Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci Kan Shaye-shaye _ Danlarabawa
- Babban Labari - Labarai

Ya Kamata Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci Kan Shaye-shaye _ Danlarabawa

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe  (Grassroot Care and Aid Foundation GCAF) Ambasada Auwalu Muhd Danlarabawa  ya yi  kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya  karshen yawaitar masu Shaye-Shayen kwayoyi a fadin Najeriya.

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe  (Grassroot Care and Aid Foundation GCAF) Ambasada Auwalu Muhd Danlarabawa  ya yi  kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya  karshen yawaitar masu Shaye-Shayen kwayoyi a fadin Najeriya.

Ambasada Auwalu Muhd ya ce akwai buƙatar a ayyana dokar ta baci akan  masu shaye-shayen miyagun kwayoyi domin yanzu lamarin ya kai dukkan masu aikata miyagun laifuka suna aikata wa ne sakamakon Shaye-Shayen kwaya wanda ya hada da taadanci, Kwacen waya, sace-sace, da daba.

Danlarabawa ya bayyana cewa daga cikin illoli da shaye-shayen kwayoyi ke yi wa Najeriya akwai haukacewa kamar yadda ake ganin matasa da kananan yara harda mata akan tituna duk sun haukace wasu suna kwana a titi da Kuma daina zuwa makaranta.

Ambasada Danlarabawa, ya kara kiia ga gwamnonin jihohin Arewa suma kowannensu ya ayyana dokar a jiharsa, hakan zai taimaka matuka gaya duba da yadda kwaya ta cutar da rayuwar matasa a Arewa maza da mata, yara da manya.

Kuma lamarin na cigaba maimakon raguwa, matukar gwamnonin suka bari aka cigaba da hakan to matsalar tsari ba zata rago ba, kullam laifika daban daban ne zasu dinga faruwa.

Idan muka duba abubuwa da ke faruwa a Arewa a yau shaye-shayen kwayoyi sune kan gaba wajen faruwar lamarin wanda ba haka ake so Arewacin kasar ya kasance ba.

Danlarabawaya ce  “Na tabbatar kowa yana kuka da wannan lamari, haka kuma nasan al’umma zasu yi farin ciki idan aka dakile lamarin, kuma a samar da wuraren gyaran hali da tarbiyya wanda zai taimakawa wadanda suka tsinci kansu a ciki a baya.

A karshe  Ambasada Auwalu Muhd Danlarabawa ya yi kira ga al’umma suma su bada gudunmawa wajen ganin sun dakile lamarin a matakin unguwanni da gidajensu da zarar sun ga ana aikata hakan su dauki matakin hanawa da kai kara, sannan masu neman kudi da lamarin a bayyana su ga hukuma domin daukar mataki a kansu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai