Home » Shugaba Tinubu Ya Ciwo Bashin Tiriliyan 50 Kawo Yanzu

Shugaba Tinubu Ya Ciwo Bashin Tiriliyan 50 Kawo Yanzu

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Gwamnatin Najeriya ta tattara haraji mafi yawa a tarihi cikin watanni 6 na 2023

A watanni 19 na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ƙididdiga ta tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ta gada.

Bashin da ake bin gwamantin Nijeriya zai ƙaru zuwa Naira tiriliyan 138 a yayin da Shugaba Tinubu ke neman amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin ƙara ciyo bashin Naira tiriliyan 1.8.

A yanzu haka ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 136, wanda idan majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo bashin Dala biliyan 2.2 daga ƙasashen waje, yawan kuɗin zai ƙaru zuwa tiriliyan 138.

Ranar Talata da ta gabata ne dai shugaba Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da takwaransa na Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen takardar buƙatar amincewarsu ya karɓo bashin.

A Wasiƙar, shugaba Tinubu ya bayyana cewa za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen da za a karɓo ne wajen cike giɓin Naira tiriliyan 9.17 da aka samu wajen aiwatar da kasafin bana (2024).

Takardar ta bayyana cewa karɓo bashin ya dace da tanadin Dokar Hukumar Kula da Basuka ta Ƙasa (DMO) ta 2003, kuma ta riga ta samu amincewar Majalisar Zartaswa ta Tarayya.

Sabon bashin na 2024 ya kai Naira tiriliyan N7.83, wanda ya ƙunshi bashin cikin gida na tiriliyan N6.06 da kuma bashin ƙasashen waje na tiriliyan N1.77.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?