Home » Yadda Ake Tuƙa Tuwon Dawa

Yadda Ake Tuƙa Tuwon Dawa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Fatima Abdullahi Shadai

Tuwon dawa ɗaya ne daga cikin jerin abincin da ake amfani da su a kasar Hausa, kuma masana kiwon lafiya suka tabbatar da ingancin cin sa. 

Yau da ikon Allah za mu kawo muku yadda ake tuƙa tuwon dawa daki-daki domin masu buƙata su koya.

Kina da ra’ayin surfa dawarki, amma dai ko ba zaki surfa ba, ki tabbatar kin tsince ta kin wanke kin shanya, kafin a kai niƙa.

ABUBUWAN DA AKE BUƘATA

1. RUWA

2. DAWA

3. KANWA

Bayan kin gama kunna wuta, sai ki ɗauko tukunya, ki tabbatar kin fara ɗaurayeta da ruwa, sannan ki zuba daidai sanwar da kike buƙata, ki ɗora akan wutar.

Daga gefe guda kuma kin tankaɗe garin dawarki, bayan ruwan ya tafasa, sai ki dama garin dawar da muciya, kada ki tsuga mata ruwa kuma ka da ki dama da kauri sosai.

Bayan kin gama dama garin, sai ki dinga zuba damammiyar dawar cikin tafasasshen ruwan kina juyawa a hankali, bayan kin gama ka da ki rufe, ki cigaba da juyawa a hankali har ya fara ƙoƙarin tafasa, sai ki rufe.

Za ki iya ƙin dama garin dawar, idan ruwan ki ya yi zafi, amma ba zafi sosai ba, sai ki ɗauko garin dawar, ki dinga warwaɗawa kina juya wa, zaki ga yana bajewa yana bin ruwan, idan ya yi zafi sosai zai dinga dunƙulewa yana gudaji, yana ƙin bajewa. Idan kinga ya fara kauri, ba kauri can sosai ba, sai ki daina waɗa garin, ki cigaba da juya shi har sai ya fara ƙoƙarin tafasa, sai ki rufe.

Ruɗen dawa yana tasowa, ki tabbatar baki yi nisa da wurin gurin ba, idan ya taso ki sa muciya kina juya shi, zai koma, yana fara dahuwa, ki ɗauko kanwa ki zuba ruwan yadda kike so ki juya.

Zaki iya zuba kanwar tun lokacin da kika yi talgen

Bayan talgen ya dahu sosai, sai ki ɗauko garin ki dinga zubawa kina juya shi, idan ya yi yadda kike buƙata sai ki cigaba da tuƙa shi har sai garin ya gama bin jikinsa, kin ji tuwon ki yana ƙara ɓas ɓas, zaki ga ya yi danƙo sosai.

Sai ki rufe ki ɗan rage wuta ki barshi ya dahu.

Bayan ya dahu aduk inda kike da ra’ayin zuba tuwon ki, sai ki kwashe ki zuba.

Girki shi ne Mace

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?