Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC

Magoya bayan tsoffin ƴan takarar shugaban ƙasa a Najeriya Peter Obi, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso sun kafa wata ƙungiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK Movement) da ta soma tattaunawa domin ganin jam’iyyar ADC ta tsayar da su takarar shugaban ƙasa da mataimaki a zaɓen 2027 da ke tafe.

Ƙungiyar, wadda aka kafa a Abuja a ranar Litinin, ta ce tuni ta soma samar da rassanta a jihohi 36 na ƙasar da Abuja, tare da naɗa shugabanninta na jihohi da yankuna domin jagorantar yaɗa ayyukanta.

Sakataren watsa labaran ƙungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya bayyana ta a matsayin gamin gambiza, don haɗa karfi da karfe tsakanin ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta Obidient Movement, da kuma ta magoya bayan Kwankwaso, wato Kwankwasiyya.

Wannan dai na nuna wani irin sabon salo na sake ɗaure ɗamara yayin da ake ta ƙulla mu’amalar siyasa, sakamakon rashin tabbacin wanda zai lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na ADC kafin babban zaɓen 2027.

Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin kungiyar ya bayyana cewa sabuwar kungiyar ta kunshi mambobi daga Kwankwasiyya, da Obidients, da jam’iyyar NNPP, da Labour da kuma wasu daga ADC.

Post masu alaƙa

An kama mutum 2 a hanyar kai wa ’yan ta’adda harsasai 314

Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami’an tsaro uziri

Hon. Idris Ɗankawu ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da sana’o’in dogaro dakai a Kumbotso