Hukumomi a Nijar sun nemi ƴan ƙasar su yi wa jami’an tsaro uziri

A jamhuriyar Nijar hukumomin tsaron ƙasar na kira ga al’ummar yankunan da ke fama da matsalolin tsaro da su yi uzuri ga dakarun ƙasar dangane da jinkirin zuwan jami’an tsaro idan aka kai hari, kamar yadda al’ummar ƙasar suka gani.

Minista tsaron ƙasar ne Janar Salifou Mody ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da kafar Television ta RTN, inda ya ƙara da kira ga yan Nijar da su fahimci cewa jami’an tsaro ba za su iya kasancewa a kowane ƙauye ba, duba da cewa Nijar na da kusan ƙauyuka 32,000.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar hare-haren ƴan ta’adda musamman a kan sojojin ƙsar.

Post masu alaƙa

An kama mutum 2 a hanyar kai wa ’yan ta’adda harsasai 314

Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC

Hon. Idris Ɗankawu ya yi alƙawarin ci gaba da ayyukan raya ƙasa da sana’o’in dogaro dakai a Kumbotso