Yan bindiga Sun Sako Mutane 45 Bayan Sulhu A Katsina

Wasu ’yan bindiga sun sako mata da kananan yara 45 da ke hannunsu a yankin Karamar Hukumar Bakori da ke Jihar Katsina.

A ranar Litinin ne ’yan bindigar karkashin jagoranci wani dan ta’adda mai suna Isiya Kwashen Garwa suka sako mutanen a yayin wani taron sulhu.

Wakilin Karamar Hukumar Bakori a Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Injiniya Abdurrahman Kandarawa ya halarci taron mika mutanen, wanda aka shirya domin shaida cewa ’yan bindigar sun rungumi zaman lafiya a karamar hukumar.

Dan majalisar ya bayyana jin dadi bisa yadda ’yan bindigar suka cika alkawarin sulhu da zaman lafiyar da aka yi da su a karamar hukumar.

A nasa jawabin, Isiya Kwashen Garwa ya yi kira ga dukkan bangarorin da suka cika alkawarin da suka dauka domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Ya kuma yi kira da a bar ’yan bindigar da aka yi sulhu da su, su rika shiga cikin al’umma ba tare da wata tsangwama ba.

Post masu alaƙa

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu

Ƴan sanda sun fara bincike kan mutuwar wanda ake zargi da sokawa matashi Wuƙa a Kano

Babachir Lawal ya fita daga ADC