Yan Boko Haram 51,828 Sun Miƙa Wuya Ga Sojin Najeriya

Kimanin ’yan Boko Haram dubu 51 da 828 sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a tsakanin watan Yulin 2021 zuwa Mayun 2022.

Babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ne ya fadi haka a yayin gabatar da wata makala a Jami’ar Edo, yana mai cewa, dubu 13 da 360 daga cikin ’yan Boko Haram din mayaka ne.

Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriyar ya kuma kara da cewa, dubu 1 da 543 daga cikin tubabbun mayakan na Boko Haram sun kammala zaman gyaran hali a sansanin Mallam Sidi tsakanin 2016 zuwa 2022, yayin da dubu 1 da 935 aka sauya musu tunani a sansanin Bulumbuktu.

A cewarsa, sojojin Najeriya sun samu jerin nasarori a yakinsu da mayakan na Boko Haram, tare da kakkabe su daga maboyarsu.

Sai dai kuma Irabor ya ce, lallai rundunar Operation Safe Corridor ta fuskanci kalubale kala-kala a yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram da suka hada da karancin kayayyaki da horo da samun goyon bayan kasa da kasa.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr