‘Yan Najeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu sun ce rayuwarsu na cikin rashin tabbas tun bayan dawowarsu.

Wani dan Najeriya mai suna James ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP rayuwarsu na cikin wani muwuyacin hali tun bayan dawowarsu kasar.
Ya kara da cewa ya tafi Afirka ta Kudu shekaru 10 da suka gabata, to amma yanzu ya dawo gida babu aikin yi.
A nata bangaren, Omotola Adeniyi, ta shaida wa AFP mahaifiyarta ce ta kai ta Afirka ta Kudu tun tana ‘yar shekara Takwas, a can tayi karatu, amma babu aikin yi, yanzu ta dawo gida ji take tamkar bakuwa a cikin kasarta.
Gwamnatin Najeriya dai ta sha alwashin tallafawa mutanen da tashe-tashen hankulan kyamar baki ya raba su da kasar da suke ci rani, amma har yanzu babu wani gwaggwaban tallafin da ya fito daga hukumomi.

Post masu alaƙa

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

Buga fasfo ne aka mayar Abuja, ba karɓarsa ba – Immigration

Hukumar ICPC ta wanke fadar shugaban Najeriya daga zargin kafa hukumar boi