Gwamnatin Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta rufe Masallacin Ibadurrahman da ke unguwar Shingen Abba a cikin garin Bauchi, sakamakon rikicin da ya shafe kusan shekaru uku yana gudana tsakanin kwamitin gudanarwar masallacin da limaminsa.
Matakin ya zo ne domin daƙile yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya janyo asarar rayuka a tsakanin al’umma.
Kwamishinan Hisba na Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar, Barrista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana wa manema labarai cewa an ɗauki wannan mataki ne bisa umarnin gwamnatin jihar tare da sahalewar kotu.
Ya ce rikicin ya daɗe yana faruwa kuma ya kai kotuna daban-daban, amma har yanzu ɓangarorin sun kasa cimma matsaya.
A cewarsa, an taɓa kai batun gaban Hukumar Shari’ar Musulunci tun shekarar 2023 inda aka yi ƙoƙarin sulhu tare da shimfiɗa dokokin zaman lafiya, amma hakan bai haifar da sakamako ba.
Ya ƙara da cewa ko da aka taɓa cire limamin masallacin na wani lokaci domin a shawo kan rikicin, bayan an dawo da shi, sai matsalar ta sake ɓarkewa.
Barrister Aminu ya jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani rikici da zai iya jefa rayukan jama’a cikin haɗari ba.
“Dokar ƙasa ta bai wa kowa dama ya yi addininsa, amma idan za a samu rashin zaman lafiya da zai kawo rikici ko rasa rai, to ba za a saka ido ba. Wannan dokar muka yi amfani da ita domin kare lafiyar al’umma muka zo muka rufe wannan Masallaci.
Ya kuma gargaɗi al’ummar yankin su bi doka, yana mai cewa duk wanda ya karya umarnin rufe masallacin zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada, har sai an samu maslahar warware rikicin.