Yan Najeriya na fuskantar ƙuncin rayuwa saboda tsadar man fetur

Farashin man fetur a Najeriya ya ƙara tashi, inda a wasu yankuna ya kai kusan N1,400 duk lita, lamarin da ke ƙara tsananta wahalhalun rayuwar jama’a.

Rahotanni sun nuna cewa tashin farashin man fetur a kasuwar duniya ne ya jawo wannan lamari, wanda ya haddasa tsadar sufuri da rayuwa gaba ɗaya.

Ko a makon da ya gabata, farashin ɗanyen mai ya kai kusan dala 120 duk ganga kafin ya sauka zuwa dala 112, lamarin da ya sa kamfanoni kamar Matatar Dangote suka ƙara farashin sayar da mai daga N1,175 zuwa N1,245 kan kowace lita.

Haka kuma, gidajen mai na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) sun ƙara farashi sau biyu cikin kwanaki kaɗan, abin da ke nuna yadda kasuwar ke fuskantar sauye-sauye.

A manyan birane kamar Legas, Kano da Abuja, direbobin haya sun ce ribarsu ta ragu, yayin da fasinjoji ke ƙara raguwa saboda tsadar kuɗin mota.

A Arewa musamman Kano, farashin ya kai har N1,390, inda wasu mazauna suka ce ana karɓar har N4,000 kan tafiyar da a baya ba ta wuce N1,000 ba.

A Abuja ma, farashin ya kai tsakanin N1,361 zuwa N1,370, yayin da a Ilorin ake sayar da shi kan N1,295 zuwa N1,343, abin da ke ƙara wa ma’aikata da iyalai ƙuncin rayuwa

A yankin Kudu kamar Fatakwal da Yenagoa, farashin ya kai N1,800, yayin da farashin sufuri ya ninka sau biyu a wasu wurare.

Manazarta sun yi gargaɗin cewa idan farashin ya ci gaba da hawa, mutane da dama za su daina amfani da motoci, yayin da harkokin kasuwanci ke ci gaba da fuskantar matsin lamba.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda