Yan sanda sun kama mutane 4 tare da ƙwato motocin sata a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum huɗu tare da ƙwato motoci uku da ake zargin sun sato a jihohin Kano da Yobe.

’Yan sandan sun ƙwato wata mota ƙirar Toyota Corolla a Katsina daga hannun wani mutum da ya ce ya saye ta kan kuɗi Naira miliyan 7.5.

Mai motar ya zargi Sale Usman, wanda aka fi sani da Dambu, da ɓatar da motar bayan ya damƙa masa ita domin ya sayar.

Haka kuma, an kama wasu mutane biyu, Abubakar Umar mai shekara 23 da Mustapha Zubairu Abdullahi mai shekara 25, bisa zargin satar wata ƙaramar mota ƙirar bas Toyota Hiace daga Kasuwar Singer da ke Kano.

’Yan sanda sun ce sun gano motar a Mariri Magadawa, cikin Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

A wani lamari kuma, rundunar ta kama Abdullahi Adamu mai shekara 40 a Kano, tare da wata motar ɗaukar kaya ƙirar Mitsubishi Canter da ake zargin an sato daga garin Potiskum na Jihar Yobe.

A cewar ’yan sanda, Adamu ya amsa laifin sato motar.

An kama shi ne a lokacin da ake shirin yi wa motar sabon fenti domin sauya kamanninta.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Kiyawa, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Post masu alaƙa

Jami’ar Azare Za Ta Bai Wa Tsohon Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Digirin Girmamawa

Najeriya ta soki harin da Houthi ta kai wa Saudiyya

Tsohon shugaban FRSC, Dauda Ali Biu, ya rasu yana da shekara 62