Yan Sanda Sun Kama Shahararren Mai Garkuwa Da Mutanen Da DSS Ke Nema

 

Jami’an tsaron hadin gwiwa na Scorpion Squad, sun sami nasarar kama shararren mai garkuwa da mutanen nan ,Sha’aibu Alhaji Ahijo, wanda hukumar tsaron farin kaya ta DSS ke nemansa ruwa a jallo.

Ahijo mai shekaru 25, an kama shi ne karkashin gadar Nyanya dake birnin tarayya Abuja, a ranar 24 ga watan Maris 2025 da misalin karfe 6:00pm na yamma bisa samun bayan sirri da jami’an tsaron suka yi.

Da yake amsa tambayoyin jami’an tsaron, ya tabbatar da cewa an kashe yaransa uku da suka hada da Musa, Babangida da kuma wani da ba a bayyana sunansa ba, a wani yunkurin garkuwa da mutane a jihar Benue.

An kama shi ne a shirye-shiryen da yake yi na sake kafa gungun masu garkuwa da mutanen a birnin tarayya Abuja.

Yanzu haka dai hukumomin tsaron sun tabbatar da cewa wanda ake zargin yana basu hadin kai wajen gudanar da bincike.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda