‘Yan sanda sun mayar da shanu 77 ga mai su a Bauchi

Rundunar ƴan sandan jihar Filato ta bayyana cewa dakarun ta sun kama shanu 77 da aka sato daga jihar Bauchi. Rundunar ta ce daga Bauchi aka kwato shanun mallakin wani makiyayi, aka kora su zuwa karamar hukumar Wase dake jihar ta Filato.

Ƴan sandan sunce  bayani suka samu cewa ƴan bindiga sun sace shannun Galadiman Yuli Duguri  daga kauyen Gajin Duguri a karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi. Ƴan sandan suka ce da hadin gwiwar ƴan banga da mafarauta suka karɓe shanun 77 suka mayar wa mai su.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Filato Okoro Alawari ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a kuma ya yi kira ga mutane su riƙa gaggauta kai wa ƴn sanda rahoton duk wani abinda ba su yarda da shi ba.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano

Mutane uku sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

CP Ibrahim Bakori ya kaddamar da sabon ofishin yan sanda a Falgore.