Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an samu raguwar manyan laifuka a jihar cikin watan Agusta 2026, sakamakon ƙara sintiri, tattara bayanan sirri da kai samame wuraren da ake aikata laifuka, tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da al’umma.
Ya ce ‘yan sanda sun kama mutane 244 bisa zargin aikata laifuka daban-daban, ciki har da masu garkuwa da mutane 8, ‘yan fashi 28, barayin motoci 7, dilolin ƙwayoyi 19 da ‘yan daba 117, yayin da aka kama wasu 65 da laifuka daban-daban.
Kwamishinan ya bayyana cewa an kwato bindigu 3 da harsasai 65, tare da kama masu safarar makamai.
Haka kuma, an kama miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da Tramadol, Diazepam, Pregabalin, Exol da Wiwi.
An kuma kwato motoci 6, keken Napep 4 da babura 7 daga hannun waɗanda ake zargi da aikata laifuka.
A wani ɓangare kuma, ‘yan sandan sun kama wani mutum da ake zargi da yin zamba ta sama da Naira miliyan 13.1, tare da kayayyaki.