Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Rundunar ‘Yan Sanda a babban birnin tarayya Abuja, ta sami nasarar gano wata budurwa da wasu da ake zargin Matsafa ne suka tsafeta a dakin Otal.
Kakakin rundunar a Abuja, SP Josephine Adeh ce ta bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar Lahadi, inda ta ce lamarin ya faru ne a ranar Jumu’ar da ta gabata, a wani dakil Otal dake yankin Wuse.
A cewar Adeh, “Jami’anmu sun isa dakil Otal din inda suke iske wata budurwa mai suna Promise Eze, ‘yar asalin jihar Ebonyi a daure a jikin kujera an manne mata baki da Bandeji harma ta fita daga hayyacin ta, hakan ne yasa suka dauke ta zuwa Asibitin gundumar Wuse inda likitoci suka ceto rayuwar ta”.
- ‘Yan Sandan Najeriya Sun Fara Aiwatar Dokar Inshorar Motoci
- Matatar Dangote Ta Rage Farashin Litar Man Fetur
Binciken mu a Otal din ya gano mana cewa kwana daya kafin faruwar lamarin, Matashiyar ta shiga dakin mutumin da ya ayyana kansa a matsayin Emmanuel Okoro daga jihar Legas.
Da take amsa tambayoyin ‘Yan Sanda, Promise ta ce sun hadu da mutumin ne a kafafen sada zumunta wanda ya ce mata sunan sa Alias Michael Prince, kuma yana aiki da wani kamfanin Mai dake jihar Delta, harma ya gayyace ta zuwa jihar Deltan amma taki zuwa wanda daga bisani suka amince su hadu a Abuja.
Bayan ta je wajen mutumin y ayi amfani da wasu abubuwa wajen yi mata wani siddabaru bayan ya raunata ta, Kafin daga bisani ya daure mata kafafuwanta da hannaye baya ga toshe mata Baki, inda ya cillata bandaki ya kulle.
Ta kuma kara da cewa kafin fitar sa taji yana waya da abokan mugun aikin nasa, inda yake shaida musu gashi nan zuwa wurin su kafin ya dawo ya karasa aikin nasa, harma ya tafi da Wayoyinta guda biyu.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja CP Olatunji Disu, ya ce tuni sun kaddamar da binciken da zai kai su ga gano wadannan bata-gari, ta yadda za’a gurfanar da su a gaban Kotu domin su fuskanci hukunci dai-dai da abinda suka aikata.
Haka kuma ya shawarci ‘yan Mata da su rika kula sosai wajen yin mu’amala da bakin fuska, harma ya bukaci dukkan mai wani rahoto na yadda zasu kama wadan da ake zargi ya tuntube su ta lambobin waya 08032003913 ko kuma 08107314192.