Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro a Arewa ta kai matakin da’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a.
Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.”
Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga.
Dambazau ya shawarci gwamnonin Arewa su kafa ma’aikatar ma’adinai a jihohinsu domin haɗa kai da hukumomin tarayya wajen sarrafa albarkatun ƙasa da ke yankunansu, don ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage talauci da kuma kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Ya kara da cewa, domin magance kashe-kashe da rashin tsaro a Arewa, dole gwamnatocin jihohi su dawo da martabar sarakunan gargajiya, su farfaɗo da harkar noma da yankin ya shahara da ita, su kuma magance matsalar yara marasa zuwa makaranta, tare da tabbatar da haɗa kan jama’a.
“Ina so in jaddada cewa sama da kashi 70 cikin 100 na masu fama da talauci sakamakon rashin tsaro suna Arewa. Tsattsauran ra’ayin addini babban barazana ne ga tsaro a yankin, wanda ya haifar da ƙungiyoyin Boko Haramnda Lakurawa da sauran ’yan ta’adda da ke addabar jama’a,” in ji shi.
- An Kammala Kilomita 39 A Titin Abuja-Kaduna-Kano – Gwamnati
- Kotu Ta Sake Dakatar Da Babban Taron PDP
Tun da fari, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya jaddada cewa batun tsaro ya shafi kowa da kowa, yana mai cewa: “Dole mu zauna tare mu tattauna yadda za mu magance wannan matsala.
“A da va haka muke ba. Najeriya ba haka take ba. Idan muka haɗa kai, muka fahimci juna, muka aiwatar da shawarwarin da muka cimma, za mu samu zaman lafiya.”
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta haɗe kai domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar ta.
“Ina damuwa da yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari a yankin Arewa maso Yamma. Ya kamata wannan taron ya nazarci tushen matsalar — watakila tana da nasaba da sauyin yanayi da wasu abubuwa,” in ji shi.
Shi ma Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya bayyana cewa taron zai bayar da dama wajen tattauna matsalolin da ke addabar Arewa tare da neman mafita mai ɗorewa ga yankin.
AMINIYA
