Daga: Safiyanu Haruna Kutama
Wata yarinya ‘yar shekara 14 mai suna, Elizabeth Peter, daga unguwar Korokpa, a karamar hukumar Paikoro a jihar Neja ta nutse a kogin Chanchaga , a lokacin da ta ke kokarin diban ruwa.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda Elizabeth ta je kogin tare da ’yan uwanta domin diban ruwa, amma ta fada cikin rami mai zurfi a cikin kogin.
Elizabeth, dalibar SS1 ce a Saint Andrew Academy, Tunga Minna, an ce tana daya daga cikin wadanda kogin ya rutsa da su.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ana samun mace-mace a duk shekara saboda ramuka ma su zurfi da ke cikin kogin, wanda ke haifar da hatsarin ga mutane da yawa.
Kawarta, Abigail Idoko, ta ce ‘’ wannan lokacin shi ne karon farko da Elizebeth ta je kogin ranar Asabar bayan ta kasa samun masu sayar da ruwa da za su saya.
Ta kuma bayyana cewa an dauki kimanin sa’o’i biyu kafin a ceto Elizabeth daga cikin ramukan da ke da zurfi.
A lokacin da majiyar mu ta ziyarci ‘yan uwan wadanda suka rasu a Korokpa, mahaifiyarta ta cika da mamaki, yayin da aka ce mahaifinta, Mista Peter, wani jami’in soji yana jihar Zamfara yana bakin aiki.