Malam El-Rufa’i Ya Koma Jamiyyar SDP

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya tabbatar da sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar zuwa jam’iyyar SDP.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ya wallafa ranar Litinin ne a shafukansa na sada zumunta.

El-Rufai ya ce, “yanzu na yanke shawarar komawa jam’iyyar Social Democratic Party, kuma zan kasance a cikin ta wajen tafiyar da al’amurana na siyasa a nan gaba.

Kwanakin baya a lokacin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, El-Rufa’i ya bayyana cewa “jam’iyyar APC ta sauka daga kan manufofin da aka assasa ta tun fil-azal.”

Ya yi zargin cewa jam’iyyar ta gaza kiran taron shugabanninta na ƙasa tsawon shekaru, wanda ya ce hakan ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

A yanzu dai wannan ya kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi na inda tsohon gwamnan zai nufa bayan raba gari da jam’iyyar APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *