Daga: Abdullahi Auwal Zubairu
Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya dakatar da yarjejeniyar musayar mai da naira tare da masu sarrafa mai na cikin gida, ciki har da matatar man Dangote da sauran masu aikin mai masu zaman kansu.
Wannan shawarar, wacce ta fara aiki nan take, ta haifar da tattaunawa game da tasirinta ga fannin makamashi na Najeriya da kuma tattalin arzikin kasar gaba daya.
Tsarin amfani da naira wajen siyan mai, wanda aka fara a ranar 1 ga Oktoba 2024, ya ba masu sarrafa mai na cikin gida damar siyan mai da naira maimakon dalar Amurka.
An kafa wannan shiri ne don tallafawa karfin sarrafa mai na cikin gida da rage dogaro da kayayyakin man fetur da ake shigo da su da rage yin amfani da kudin waje.
Dakatar da yarjejeniyar yana nufin cewa masana’antun sarrafa mai na Najeriya, kamar matatar man Dangote , yanzu za su sami mai daga masu samarwa na kasa da kasa, inda za su biya da dalar Amurka maimakon naira.
Ana sa ran wannan sauyi zai kara yawan farashin , wanda zai iya haifar da karuwar farashin man fetur a kasuwa.
Bisa ga majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin, NNPC ta sanar da masu sarrafa mai na cikin gida cewa ta riga ta ware samar da mai don kwangiloli na gaba, wanda hakan ya sa babu isasshen mai ga masana’antun sarrafa mai na cikin gida.
Wannan bayani ya zo duk da rahotannin cewa samar da mai na Najeriya ya karu tun lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki.
Dakatarwar ta haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki musamman ga matatar Dangote wadda ke shirin zama daya daga cikin manyan matatun sarrafa mai a Afirka.
Sauran masu sarrafa mai masu zaman kansu, ciki har da Waltersmith Petroman da BUA Refinery, suma abun zai shafe su .
Masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa dakatarwar na iya shafar tattalin arzikin Najeriya, kuma Naira za ta ci gaba da karyewa a idon duniya.
- Atiku Ya Bayyana Matsayarsa Kan Cigaba Da Zama A PDP
- Za A Yi Sabbin Manyan Makarantu 5 A Zaria A 2025 – Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya