Yau Majalisar Dattawa za ta tantance sabon Ministan Tsaro

Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele.

Sanarwar ta ce majalisar ta karɓi buƙatar Shugaban Ƙasa Tinubu na tabbatar da wanda aka naɗa Ministan Tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa za a karanta wasikar a gaban majalisar a ranar Laraba, sannan kuma za a ci gaba da tantance wanda aka naɗa nan take.

Opeyemi ya bayyana cewa majalisar ba za ta iya jinkirta irin wannan buƙata ba a wannan lokaci mai muhimmanci, domin ta shafi muhimman abubuwan da suka shafi ƙasar.

A ranar Talat ace Tinubu ya aike da sunan Christopher gaban majalisar domin amincewa bayan murabus din tsohon Ministan, Muhammad Bdaru Abubakar.

Kafin nadin nasa dai, Christopher shi ne tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya da Tinubu ya sauke tare da ragowar manyan hafsoshi a kwanakin baya.

Post masu alaƙa

Babbar alkalin Kano ta rantsar da sabbin alkalan kotunan shari’a su 30

Ba za mu buɗe Hormuz ba sai Amurka ta buɗe tashar ruwanmu – Iran

Jirgin ‘yan cirani ya kife a tekun Libiya