Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce rundunar za ta ƙarfafa matakan tsaro gabanin zaɓen 2027, tare da tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaɓen da kuma bayan kammala shi.
Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin kwamishinan.
Sanarwar ta ce, CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara na kungiyar masana hulɗa da jama’a ta Najeriya (NIPR), reshen Jihar Kano, wanda aka gudanar a ranar Asabar a Kano, mai taken taken rawar da jami’an yaɗa labarai ke takawa wajen tafiyar da sakamakon zaɓe.
Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya da jita-jita na iya haddasa tashin hankali tare da raunana amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
Ya ce rundunar ta fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki, ciki har da matasa, ’yan siyasa da ’yan jarida, domin wayar da kansu kan muhimmancin zaman lafiya.
Ya kuma ce za a ci gaba da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen dakile dabar siyasa da sauran abubuwan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.
A nasa ɓangaren, kwamishinan zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a Kano, Ambasada Zango Abdu, ya ce hukumar na shirin gudanar da zaɓen 2027 cikin ’yanci, adalci da sahihanci.
Sanarwar ta ce mahalarta taron sun kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, INEC, gwamnati da kafafen yaɗa labarai domin gudanar da zaɓe cikin lumana.