Gabanin bikin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya , kungiyar #TakeItBackMovement ta ce za ta gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa, muguwar gwamnati da rayuwa mai tsanani gobe Alhamis, 12 ga Yuni 2025 a jihohi 20.
A jiya Talata ne dai ƙungiyar da ta shirya zanga-zangar ta bayyana wuraren da ake sa ran za a taru domin bayyana ƙorafin ‘yan Najeriya.
A bana Mulkin Dimokuraɗiyya ke cika shekaru 26 ba tare da katsewa ba a Najeriya.
Masu shirya zanga-zangar sun ce zanga-zangar adawa da wahalhalu, rashin tsaro da kuma “Rikirkicewar al’amurra” a ƙarƙashin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kodinetan kungiyar na kasa Juwon Sanyaolu, ya bayyana cewa za a gudanar da zanga-zangar a akalla jihohi 20.
Daga cikin Jihohin akwai:
Ondo
Abuja
Bauchi
Ibadan
Osun
Delta
Adamawa
Lagos
Naija
Edo da sauransu.
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Gobarar Kasuwar Farm Centre
- Ana Zargin Miji Ya Halaka Amaryarsa A Gwarzo
Sanyaolu ya ce an shirya gudanar da zanga-zangar ne a ranar 12 ga watan Yuni domin ta zo daidai da ranar Dimokuradiyyar Najeriya a matsayin wata alama ta kira ga rikon amana da mutunta ka’idojin dimokuradiyya.
“Bukatunmu a bayyane su ke, ranar 12 ga watan Yuni wata dama ce ga ‘yan Najeriya na neman shugabanci nagari da rikon amana cikin lumana.
“Kundin tsarin mulki ya bayyana ƙarara cewa jin dadin jama’a da tsaron lafiyar su ne babban aikin gwamnati, kuma waɗannan ayyukan sune wadanda gwamnatin Tinubu ta kasa.”
Shugaban ƙungiyar da ke shirin yin zanga-zangar ya buga misali da rahoton da Amnesty International ta fitar, rahoton da ya yi zargin cewa sama da ‘yan Najeriya 10,000 ne suka rasa rayukansu a sakamakon matsalolin tsaro iri daban-daban tun bayan hawan shugaba Tinubu.
“Sama da ’yan Najeriya miliyan 133 ne ke rayuwa cikin talauci, da yawa talauci ya tilasta musu barin gidajensu, ga rashin tsaro.
An ce Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihohin Legas, Ogun da Neja sun tsaurara matakan kariya domin ta tabbatar da zaman lafiya gabanin ranar dimokradiyyar.
Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da rundunar ‘yan sandan shiyya ta biyu, Adegoke Fayoade, ya ce an umurci kwamishinonin ‘yan sanda da su tabbatar da ingantaccen tsaro kafin, da kuma bayan ranar Alhamis, wato ranar da za a yi bikin Ranar anar Dimokuradiyya.