Za A Samu Fari A Jihohi 9 Na Arewacin Najeriya A Tsakiya Daminar 2025

Hukumar da ke lura da yanayi a Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za a samu fari mai tsananin gaske a jihohi tara na Arewacin Najeriya a daminar bana. 

Ta ce farin zai iya kai wa tsawon kwanaki 21, a tsakiyar damina daga tsakanin watan Yuni zuwa Watan Agusta a shekarar 2025.

Ana sa ran farin zai shafi jihohin Maiduguri, Gombe, Yobe, Filato, Jigawa, Kano, Zamfara, Sakkwato da kuma jihar Kebbi.

Masana harkokin noma a Najeriya sun shawarci manoma da masu saka hannun jari a fannin noma da su nemi shawarar masana kan yadda ya kamata su yi, domin kaucewa asara mai yawa.

Ko a tsakayar daminar bara ma dai an samu irin wannan fari a jihar Filato, Taraba da wani yanki na jihar Adamawa, abin da ya janyo ƙarancin abinci a kakar bara a waɗan nan yankunan.

Post masu alaƙa

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu