Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta bukaci matasa su nisanci zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a fadin kasar.
Shehu Muhammad Makarfi da ya wakilci majalisar a wajen taron bita na kwanaki biyu da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya mai taken “Dogaro da Kai da Kame Kai: Mafi Girman Dabara ga Malamai a cikin Da’awa” a Gombe ne ya bayyana hakan.
Makarfi ya ce duk wanda ke karfafa wa matasan Najeriya guiwa su yi zanga-zanga, ba ya neman maslaha ga kasa.
Ya ce, “Zanga-zanga koma-baya ce ga Najeriya, musamman a Arewaci inda muke jin dadin zaman lafiya.
- Za Mu Bada Kariya Ga Masu Zanga-zanga -I.G
- Dambarwar Matatar Man Dangote Babbar Matsalace-Atiku Abubakar
Shehin malamin ya jaddada bukatar kauracewa zanga-zangar in da ya ce “Ba za mu bari bata-gari su tarwatsa zaman lafiyarmu ba,” ya jaddada.
Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Gombe, a matsayin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, da ya dauki matakai don hada malamai da sarakuna wajen karfafa zaman lafiya da yi wa jama’a gargadi kan hadarin zanga-zanga.