• Home  
  • Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran
- Babban Labari

Za mu kai hari kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila – Iran

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar kai hare-hare kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila da ke yankin. Mai magana da yawun hedikwatar, Ebrahim Zolfaghari, ya ce wannan mataki na ramuwar gayya ne inda ya zargi Amurka da Isra’ila da kai hare-hare […]

Hedikwatar Khatam al-Anbiya, wacce ita ce babbar cibiyar da ke kula da daidaita ayyukan rundunonin sojin Iran, ta yi barazanar kai hare-hare kan gidajen jami’an Amurka da Isra’ila da ke yankin.

Mai magana da yawun hedikwatar, Ebrahim Zolfaghari, ya ce wannan mataki na ramuwar gayya ne inda ya zargi Amurka da Isra’ila da kai hare-hare kan gidajen fararen hula a birane daban-daban na Iran.

A cewarsa, hare-haren da ake kai wa Iran sun haddasa asarar rayukan manyan kwamandojin soja da jami’ai a lokacin rikicin.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da Ali Khamenei, tsohon jagoran addinin Iran, wanda rahotanni suka ce an kashe shi a hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta barkewar yakin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai