Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-rufa’ ya bayyana cewa a shirye ya ke ya rantse da Al’ƙur’ani akan bai saci ko sisi daga asusun gwamnatin Jihar Kaduna ba.
El’rufai ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawarsa da ‘ƴan jarida
El’rufa’i wanda shine gwamnan jihar kaduna daga shekarar 2015 zuwa 2023 ya bayyana cewa bai shiga gwamnati dan ya azurta kansa ba, sai dai domin ya hidimtawa al’umma.
A baya-bayan nan ne dai majalisar jihar Kaduna ta zargi El-rufa’I da karkatar da tsabar kudi har Naira Biliyan ɗari huɗu da arba’in da uku a lokacin da yake gwamnan jihar.
To sai dai El’rufa’I da muƙarraban gwamnatin sa na wancan lokacin sun musanta wannan zargi, inda suka bayyana shi amatsayin zance mara tushe balle makama.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa da Zarar ya kammala karatunsa zai dawo fagen siyaysa domin cigaba da hidimtawa al’umma.