Home » Zanga-zanga: Jami’an Tsaro Sun Kafa Shingayen Bincike A Wajen Abuja

Zanga-zanga: Jami’an Tsaro Sun Kafa Shingayen Bincike A Wajen Abuja

Rundunar sojin da ke tsaron shugaban ƙasa da ’yan sanda sun kafa shingayen bincike a manyan hanyoyin shiga Abuja da fata Abuja.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Rundunar sojin da ke tsaron shugaban ƙasa da ’yan sanda sun kafa shingayen bincike a manyan hanyoyin shiga Abuja da fita daga birnin.

Matakin ya biyo bayan zanga-zangar neman a sako jagoran ƙungiyar ta’addanci ta IPOB, masu neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu.

Zanga-zangar na zuwa ne a yayin da ake zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, har aka tsare wasu manyan sojoji aƙalla 16 da ake zargin wani tsohon gwamna ya ɗauki nauyinsu juyin mulkin suka shirya aiwatarwa.

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta zargin alhali wasu majiyoyi masu tushe sun tabbatar mana da gaskiyar zargin yunƙurin.

A safiyar Litinin ɗin nan ne Omoyele Sowore, jagoran tafiyar #RevolutionNow, ya jagoranci zanga-zangar neman sakin Nnamdi Kanu a sassan Abuja.

Zanga-zangar ta haddasa cunkoson ababen hawa a wurare da dama da suka hada da yankin Bwari, Zuba, Nyanya da sauran hanyoyin shiga birnin Abuja.

Musamman, an rufe hanyar da ke haɗa Bwari da Tsakiyar Birni a yankin War College da ke Ushafa, da kuma Dutse-Sokale, abin da ya sa ma’aikatan gwamnati da dama suka maƙale a hanya.

Da fari, jami’an tsaro sun taƙaita tsauraran matakai ne a wuraren da suka haɗa da Fadar Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya, Kotun Daukaka Kara, Hedikwatar ’Yan Sanda ta Kasa, da kuma Dandalin Eagle Square.

Sai dai wata majiya daga hukumar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa faɗaɗa shingayen zuwa unguwannin da ke wajen birnin ya zama dole domin hana “’yan kutse daga waje” shiga cikin birnin.

Wani jami’in tsaro ya kuma bayyana cewa bayanan sirri sun nuna masu zanga-zangar na sake tsara dabaru tare da yiwuwar shigo da wasu matasa zauna-gari-banza domin tayar da da tarzoma.

Wani ma’aikacin gwamnati, Isaac Babalola, ya shaida wa wakilinmu cewa ya koma gida bayan ya maƙale na tsawon lokaci a cunkoson motoci a kusa da War College Camp da ke Ushafa.

Haka kuma, wasu direbobi da suka taso daga Mararaba–Nyanya sun bayyana takaici, suna cewa sun karaya saboda ba su shirya irin wannan tsaiko ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?