• Home  
  • Zazzaɓin Lassa Ya Halaka Mutane 176 A Jihohin Najeriya 21
- Babban Labari - Labarai

Zazzaɓin Lassa Ya Halaka Mutane 176 A Jihohin Najeriya 21

Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 176 sakamakon cutar zazzaɓin Lassa a faɗin jihohin ƙasar 21 cikin wata 10. NCDC ta ce adadin mutanen da cutar ke kashewa ya ƙaru daga kashi 16.6 cikin 100 a 2024 zuwa 18.4 a 2025 duk da raguwar masu kamuwa […]

Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 176 sakamakon cutar zazzaɓin Lassa a faɗin jihohin ƙasar 21 cikin wata 10.

Hukumar ta ɗora alhakin mutuwar kan rashin kai rahoto da wuri, da rashin neman taimakaon likitoci.

Kazalika, ƙarin mutum 955 ne daga cikin 8,367 da aka gwada suka kamu da cutar ta Lassa a 2025, inda jihohin Ondo, Bauchi, Edo, Taraba suka zama cibiyar cutar da kashi 88 cikin 100 na duka mutanen.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000