Ƙungiyar mafarauta ta Nijeriya, zata gudanar da zanga-zangar lumana saboda, rashin biyan diyya ga iyalan mafarauta yan asalin jihar Kano, da aka yi wa kisan gilla a Uromin jihar Edo.
Akallla mafarauta 16 aka yi wa kisan gilla lokacin da suke hanyarsu ta dawowa gida Kano daga kudancin Nijeriya, lamarin da ya jefa iyalansu cikin kunshin rayuwa, bayan gaza cika musu alkawarin da gwamnatin Kano, ta yi musu na karɓo musu diyyar waɗanda aka kashe, a wajen gwamnan jihar Edo.
Watanni goma sha ɗaya kenan da kisan mafarautan, a karamar hukumar Uromin jihar Edo, inda gwamnan jihar Lucky Opkebolo, ya yi alƙawarin biyansu diyya amma har yanzu ba a cika alƙawarin ba.
Sai dai matan mamatan da Iyayensu sun bayyana halin kuncin rayuwar da suke ciki, na kula da marayun da aka barmusu.
Ibarhim isah, wanda ya tsallake rijiya da baya , ya bayyana cewa tun lokacin da abunda ya faru aka yi alƙalrin biyan diyyar amma har yanzu babu ba a biya, ko kuma ɗaukar matakin shari’a akan waɗanda zargin.
Ƙungiyar mafarautan ta ce ranar 21 ga watan Fabarairun 2026 zata gudanar da zanga-zangar , a birnin tarayya Abuja sannan ta dawo jihar Kano, ranar 27 ga watan don ci gaba da zanga-zangar matukar ba a biya diyyar ba.
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 16, sun ceto mutum 11 da aka sace a Borno
- Abin da Bala Kaura ya ce kan rade-radin sauya shekarsa zuwa APC
Dagacin garin Torankawa dake ƙaramar hukumar Bunkure a jihar Kano, Alhaji Ado Ali, ya ce gwamnatocin jahihin Edo da Kano babu wani abu da suka bawa iyalan mamatan sai alƙawarin da ba a cika ba.
Ya ƙara da cewa ƴan siyasar da suka taimaka musu , sune sanatan kano ta Arewa ,Sanata Barau I Jibrin da sanatan kano ta Kudu, Sanata Abdurraham Kawu Sumaila da ɗan majalissar tarayya mai wakiltar Rano, Bunkure da Kibiya da kuma ɗan majalissar jiha mai wakiltar Bunkure.
A ƙarshe sun buƙaci gwamnatin jihar Kano, data bibiyi wannan lamarin kan haƙƙin nasu wajen gwamnan jihar Edo.

