• Home  
  • Ɗalibar Jami’ar IBB Ta Faɗi Ta Rasu
- Babban Labari - Labarai

Ɗalibar Jami’ar IBB Ta Faɗi Ta Rasu

Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya. Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar. Rahotanni sun ce ta fara […]

Wata ɗalibar aji biyu a sashen nazarin ƙwayoyin halittu da sunadarai na Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU), Lapai da ke Jihar Neja ta riga mu gidan gaskiya.

Aminiya ta ruwaito cewa, Fatima Adamu Muhammad, ta rasu ne bayan ta yanke jiki ta faɗi a wani matsuguninta da ke wajen makarantar.

Rahotanni sun ce ta fara ƙorafin cewa ba ta jin daɗin jikinta da alamu na rashin lafiya, inda daga daga bisani ta yanke jiki ta faɗi.

Sai dai bayan an garzaya da ita asibitin gwamnati na Lapai, likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi mata halinsa.

Mahukunta sun tabbatar da rasuwar ɗalibar da aka bayyana a matsayin babban rashi ga iyalai, makusanta da al’ummar jami’ar.

Wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na jami’ar, Alhaji Baba Akote, ya fitar, ya bayyana cewa ɗalibar tana da nutsuwa sannan mai hazaƙa ce da ladabi ga malamanta da kuma faran-faran a cikin ’yan uwanta ɗalibai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai