Shugabar Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya Cindy McCain, ta ce a faɗin duniya mutane miliyan 700 ne ba su da tabbacin samun abinci kullum, yayin da buƙatar abincin ke ƙaruwa.
Cindy McCain ta shaida wa Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya a jiya Alhamis cewa rashin isassun kuɗi sun tilasta wa hukumarta rage tallafin abincin da take bai wa miliyoyin mutane, kuma tace za a ci gaba da ragewa.
Tace suna fama da rikice-rikice iri-iri masu tasiri a yanzu, waɗanda za su ta’azzara matsalar jin-ƙai a duniya. Cindy McCain tace wannan shi ne ainihin abin da ke faruwa a zahiri, ta ƙara da cewa akwai kuma waɗansu tashe-tashen hankulan da sai nan gaba za a ga tasirinsu a duniya.
Shugabar Hukumar Samar da Abincin Ta Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ƙiyasta cewa kusan mutane miliyan 47 a ƙasashe fiye da 50 na dab da faɗawa cikin tsananin yunwa, kuma tace yara miliyan 45 ƴan ƙasa da shekara biyar na fama da tamowa.
A cewar Hukumar, a ƙasashe 79 da take gudanar da ayyukanta kimanin mutane miliyan 783 suna kwana da yunwa kullum, wato kashi ɗaya cikin 10 na yawan mutanen duniya na kwanciya ba tare da sun samu abin sakawa a bakinsu ba.
Hukumar ta ce fiye da mutane miliyan 345 na fuskantar matsanancin ƙarancin abinci a wannan shekarar, wato an samu ƙarin mutane miliyan kusan 200 ke nan daga farkon shekarar 2021 kafin annobar cutar Korona.
Hukumar ta ce rikice-rikice da taɓarɓarewar tattalin arziki da sauyin yanayi da tashin farashin takin zamani ne suka ta’azzara matsalar ja’ibar yunwa a duniya.