Ƙungiyoyin ƙwadago sun bayyana dalilin da ya sanya ba su halarcci taron da gwamnatin tarayya ta kira su ba.
Kingiyoyin sun bayyana cewa gwamnatin ba ta aike musu da takardar sanarwar taron ba a kan lokaci Ƙungiyoyin ƙwadagon dai na shirin fara yajin aikin sai baba-ta-gani a faɗin ƙasar nan a ranar, 3 ga watan Oktoba
Taron da gwamnatin tarayya ta kira tare da shugabannin ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), da ƙungiyar ƴan kasuwa ta kasa (TUC), bai yiwu ba.
Gwamnatin tarayya ta gayyaci shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon biyu domin yin wani taro a jiya Juma’a a fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja, kan yajin aikin da suke shirin farawa.
Wata majiya mai tushe tace ƙungiyar kwadagon ta bayyana cewa sanarwar taron da ta fito daga ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, ta same ta ne da misalin ƙarfe 10 na safiyar Juma’a, lokacin bai fi saura sa’o’i biyu a fara taron ba kamar yadda aka tsara.